Bangaren kasa da kasa, An fara gudanar da wani shiri na horar da masu bukatar harder kur'ani mai tsarki a birnin Nuwakshut na kasar Mauritaniya, wanda cibiyar kula da ayyukan jin kai da bunkasa ilimi ta kasar ta dauki nauyin shiryawa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ami an bayyana cewa, an fara gudanar da wani shiri na horar da masu bukatar harder kur'ani mai tsarki a birnin Nuwakshut na kasar Mauritaniya, wanda cibiyar kula da ayyukan jin kai da bunkasa ilimi ta kasar ta dauki nauyin shiryawa a birnin.
Bayanin ya ci gaba da cewa aiwatar da wannan shiri yana da matukar muhimamnci ga masu bukatar hardar kur'ani, da kuma wadanda suke bukatar shiga gasar hardar kur'ani mai tsarki a mataki na kasa ko kuma a mataki na kasa da kasa.
Yanzu haka daruruwan dalibai da matasa masu sha'awar hardar kur'ani mai tsarki ne suka yi rijistar sunayensu a wannan cibiya, inda ake sheda musu sharudda da ka'idoji na cibiyar domin samun masaniya kan ayyukanta.
705551