IQNA

Za A Gudanar Da Tarukan Ranar Ali Asghar (AS) Ta Duniya

12:18 - December 05, 2010
Lambar Labari: 2042070
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da tarukan ranar Ali Asghar a matsayi na duniya a cikin mako mai zuwa, wanda ya yi daidai da ranar daya ga watan muharram watan iyalan gidan manzon Allah (SAW) suka shahada tare da imaminsu.



Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga wani shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, za a gudanar da tarukan ranar Ali Asghar a matsayi na duniya a cikin mako mai zuwa, wanda ya yi daidai da ranar daya ga watan muharram watan iyalan gidan manzon Allah (SAW) suka shahada tare da imaminsu amincin Allah ya tabbata a gare shi.

An gudanar da irin wadanan taruka masu albarka ashekarar da ta gabata a birane na kasashen duniya daban-daban, da suka hada da Iraki, Saudiyya, Iran, Bahrain, Kuwait, Qatar, Austaralia, Oman, India, Pakistan, Afghanistan, Syria, Lebanon, Canada, Faransa, Thailand, Danmark, Amurka da dai sauransu.

Watan Muharram wata mai tattare da tarihin na masifu da bala'oi da iyalan gidan manzon Allah (SAW) suka gain a cikin tarihinsu, sakamakon tsayawa kan sahihin tafarki na ma'aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka.

706038



captcha