Bangaren kasa da kasa, Babban sakataren kwamitin kula da harkokin bunkasa ilimi da al'adun muslunci Abdulaziz Tuwaijari, ya halarci zaman taron da ake gudanarwa abirnin Paris na kasar Faransa, dangane da batutuwa da suka danganci iyalai.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo mallakin kungiyar ISESCO an bayyana cewa, babban sakataren kwamitin kula da harkokin bunkasa ilimi da al'adun muslunci Abdulaziz Tuwaijari, ya halarci zaman taron da ake gudanarwa abirnin Paris na kasar Faransa, dangane da batutuwa da suka danganci iyalai daga sassa daban-daban na duniya.
Zaman taron taron dai ya samu halartar wakilai daga kungiyoyi da cibiyoyi daban-daban da suke gudanar da ayyuka da suka danganci iyalai a kasashen duniya, inda ake tattauna matsaloli da suka shafe su da kuma hanyoyin warware su daga mahang daban-daban.
Abdulaziz Tuwaijari ya gabatar da jawabi a gaban taron, inda ya bayyana cewa a wannan zamanin da muke rayuwa an samu gagarumin ci gaba da fuskacin fahimtar rayuwa ta zamantakewa atsakanin iyalai na al'ummomin duniya.
706091