IQNA

Za A Gudanar Da Taro Kan Tattalin Arziki A Mahangar Musulunci A Turkiya

12:16 - December 05, 2010
Lambar Labari: 2042073
Bangaren kasa da kasa, Za agudanar da wani zaman taro da zimmar yin nazari kan muhimman batutuwa na harkokin tattalin arziki da kuma mahangar addinin muslunci a kansu a kasar Turkiya, wanda kwamitin masana harkokin tattalin arziki na kasar ya shirya gudanarwa.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na dunya bultini an habarta cewa, za agudanar da wani zaman taro da zimmar yin nazari kan muhimman batutuwa na harkokin tattalin arziki da kuma mahangar addinin muslunci a kansu a kasar Turkiya, wanda kwamitin masana harkokin tattalin arziki na kasar ya shirya gudanarwa a cikin mako mai zuwa.

Bayanin ya ci gaba da cewa za a gudanar da zaman taron a ranar Asabar mai zuwa da kimanin karfe 11 na rana, tare da halartar mambobin kwamitin masana tattalin arziki na kasar Turkiya, gami da malaman jami'oi da kuma wasu daga cikin mambobin majalisar dokokin kasar.

Taron zai mayar da hankali ne wajen yin bahasi kan yadda za a iya yin amfani da mahangar muslunci wajen warware da dama daga cikin matsaloli na harkokin tattalin arziki a matsayi na kasa har ma a matsayi na duniya.

705988




captcha