Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na muhit an bayyana cewa, ana ci gaba da gudanar da wani zaman taro da aka shirya a birnin Alkahira na kasar Masar a mataki na kasa da kasa domin bahasi kan sirar ma'aki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka a jami'ar birnin.
Wannan zaman taro dai yana samun halartar manyan malamai da masu nazari gami malaman jami'oi na kasar da ma kasashen ketare, inda suke yin bahasi kan sirar manzon Allah (SAW) kamar yadda ya zo a cikin tarihin mulunci, da irin darussan da al'ummomin musulmi za su iya dauka daga dukkanin rayuwa ta ma'aiki (SAW)
Daga cikin kasashen da ke halartar taron sun hada da Saudiyya, Masar, Sudan, Kuwait, India, Amurka. Taron dai yana dogara da abubuwan da suka zo cikin nassi da kuma abin da masana tarihi suka rubuta dangane da sirar ma'aik (SAW)
706887