IQNA

An Watsa Rahoton Matakan Nuna Wariya Kan Musulmi

13:26 - December 06, 2010
Lambar Labari: 2043172
Bangaren kasa da kasa; cibiyar bincike ta musulmin Yammacin Turai dake da matsugunninta a jami'ar Exeter a Britaniya ta watsa rahotonta daga birnin London mai sunan matakan nuna wariya kan musulmi a London.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta sociorel ya watsa rahoton cewa; cibiyar bincike ta musulmin Yammacin Turai dake da matsugunninta a jami'ar Exeter a Britaniya ta watsa rahotonta daga birnin London mai sunan matakan nuna wariya kan musulmi a London. Wannan rahoto ya kumshi shafika sattin da daya da malaman jami'ar suka rubuta dam asana masu bincike a cibiyoyin nazari na musulmi a Turai suka watsa marubuta wannan rahoto sun yi nuni da yadda hadarin da ke nuni da yaduwa da karuwar masu tsananin nuna adawa da kiyaya kan musulmi da Musulunci a Britaniya tare da bukatar gwamnati da ta dauki kwararan mataka na yakar wannan matsala ta nuna adawa da kyama kan addinin Musulunci. Rahoton ya maida hankali kan guraren da aka fi takurawa da cin fuska da nunawa musulmi wariya a kasar kama daga gurarai irin su makarantu,jami'o'I cibiyoyin ilimi, guraren taruwar jama'a kamar su asibici da cewa matsalar kullum kara kamari take yi kuma ana bukatar daukan mataki na gaskiya.


706628
captcha