IQNA

Azhar Za Ta Bude Cibiyar Koyar Da Larabci Ta Kasa Da Kasa

16:50 - December 06, 2010
Lambar Labari: 2043353
Bangaren kasa da kasa; komitin koli na jami'ar Azhar ya amince da bude wata cibiya ta kasa da kasa ta koyar da harshen larabci ta musamman ga wadanda ba larabawa ba da zummar yada harshen kur'ani.

Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta Muhit ya watsa rahoton cewa; komitin koli na jami'ar Azhar ya amince da bude wata cibiya ta kasa da kasa ta koyar da harshen larabci ta musamman ga wadanda ba larabawa ba da zummar yada harshen kur'ani.Abdul Da'im Alnasir mai bada shawara ga sheikhul Azhar dangane da wannan labari ya bayyana cewa; wannan cibiya wani sabon abin jinjinawa ne ga jami'ar Azhar na yada yaren kur'ani mai girma a fadin duniya kuma a nan gaba za a bude reshen wannan cibiya a kasashe daban daban kuma da daman a duniya.


706646
captcha