IQNA

An Rattaba Hannu Fahimtar Juna Tsakanin ISESCO Da Cibiyar Iyali A Faransa

14:05 - December 07, 2010
Lambar Labari: 2043464
Bangaren kasa da kasa, An rattaba hannu tsakanin cibiyar bunkasa harkokin ilmi da ala'dun muslunci ta kasa da kasa ISESCO kan fahimtar junada gunar da wasu ayyuakan hadin gwiwa da cibiyar kula da harkokin iyali ta kasar faransa.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa da hulda da jama'a na ISESCO an bayyana cewa, an rattaba hannu tsakanin cibiyar bunkasa harkokin ilmi da ala'dun muslunci ta kasa da kasa ISESCO kan fahimtar junada gunar da wasu ayyuakan hadin gwiwa da cibiyar kula da harkokin iyali ta kasa da kasa.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan yarjejeniya tana da matukar muhimmanci ga dukkanin bangarorin biyu, domin kuwa suna taka gagarumar rawa dukkaninsu a matsayi na kasa da kasa wajen warware da dama daga cikin matsaloli na zamantakewar al'umma.

Sa hannu kan yarjejeniyar dai ya zo bayan kamala wani zaman taro da cibiyar kula da harkoki iyalai da ked a cibiyar a kasar Faransa ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa, inda aka gayyaci bababn sakataren cibiyar ta ISESCO Al-tuwaijari.

707431




captcha