IQNA

Za A Gudanar Da Wani Zama Kan Palastinu A Birnin Paris Na Faransa

14:05 - December 07, 2010
Lambar Labari: 2043465
Bangaren kasa da kasa, Za a gudanar da wani zama na musamamn da zai yi dubi kan halin da ake ciki a yankin palastinu ta bangaren siyasa da tattalin arzikin alummar yanki, wanda za a gudanar a birnin paris fadar mulkin kasar Faransa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ehess cewa, za a gudanar da wani zama na musamamn da zai yi dubi kan halin da ake ciki a yankin palastinu ta bangaren siyasa da tattalin arzikin alummar yanki, wanda za a gudanar a birnin paris fadar mulkin kasar Faransa a cikin makon nan.

Zaman taron dai zai samu halartar masana daga sassa daba-daban na kasar faransa, daga cikin mahalartan hard a masana da kuma malaman jami'oi gami da wakilan kungiyoyin musulmi da na larabawa mazauna a kasar, gami da wakilan kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa.

Yanzu dai cibiyar kula da harkokin bincike ta ehess wadda ita ce ta dauki nauyin shirya taron ta bayyana cewa ta kamala dukkanin shirye-shiryenta na daukar nauyin gudanar da wannan babban taro a matsayi na kasa da kasa a birnin na Paris.

707404





captcha