Bangaren kasa da kasa, Za a gudanar da gasar rubutu ta duniya kan rayuwar Imam Amirul muminin (AS) da za a bayar da babbar kyauta a kanta a birnin Najaf Ashraf, da nufin kara fitar da wasu daga cikin boyayyun ilmomi da suka shafi rayuwarsa mai albarka.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Nun cewa, za a gudanar da gasar rubutu ta duniya kan rayuwar Imam Amirul muminin (AS) da za a bayar da babbar kyauta a kanta a birnin Najaf Ashraf, da nufin kara fitar da wasu daga cikin boyayyun ilmomi da suka shafi rayuwarsa mai albarka.
Wannan gasa za ta tabo muhimman lamurra da suka danganci rayuwarsa ta fuskacin ilmi, hikima, iya jagoranci, matsayi a wajen manzon Allah da dai dukkanin abubuwan da ya kamata a fada bincike kansu dangane da rayuwarsa domin amfanin sauran al'ummomin muslmi da ma al'ummomin duniya baki daya.
Yanzu dai an fara samun wadanda suka bayyana shirinsu na shiga wannan gasa, inda za su bayar da abubuwa da suka rubuta bayan gudanar da binike mai zurfi kan rayuwarsa, kuma za a sanar da ranar karbar rubuce-rubucen a nan gaba.
707379