IQNA

Ayatollah Sistani Lamuni Ne Ga Hadin Kan Musulmin Kasar Iraki

12:54 - December 08, 2010
Lambar Labari: 2044616
Bangaren kasa da kasa, Shugaban majalisar dokokin kasar Iraki Usama Najafi ya bayyana cewa, babban malamin addinin kasar Iraki Ayatollah Sistani shi ne babban lamuni ga dukkanin hadin kan da ake bukata tsakanin al'ummar kasar.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na Nun an bayyana cewa, shugaban majalisar dokokin kasar Iraki Usama Najafi ya bayyana cewa, babban malamin addinin kasar Iraki Ayatollah Sistani shi ne babban lamuni ga dukkanin hadin kan da ake bukata tsakanin al'ummar kasar ta Iraki.

Usama Nafi ya bayyana hakan ne bayan kammala wata ganawa da ta hada shi da Ayatollah Sistani a gidans da ke birnin Najaf, wanda ya sheda masa cewa ya zama wajibi a kan dukkanin bangarorin siyasarsa day a rataya kansu su kafa gwamnati su gaggauta safke wannan nauyi da ya rataya a kansu.

Yanzu haka dai bayan kallafawa fira ministan kasar Iraki Nuri maliki nauyin kafa gwamnati, dukkanin banagarorin siyasa na ci gaba da gudanar da shawarwri kan hakan.

708314




captcha