Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga majiyar liveepool-shia ya watsa rahoton cewa; an fara gudanar da bukuwan juyayin ranekun muharram a birnin Manchestar na kasar Britaniya kuma tun ranar sha biyar ga watan azar ne na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara aka fara. Irin wadannan bukukuwa za a ci gaba da gudanar da su har zuwa ranar ashirin da shida na wannan wata kuma a kowa ce rana za a fara daga karfe bakwai na yamma zuwa tara da rabi na dare kuma bayan kammala sallar jama'a ta magariba da isha'I za a fara gudanar da jawabai da wa'azi da bayanai kan abubuwan da suka fara da kuma suka haddasa shahadar imam Huseini (AS) da sahabbansa da iyalan gidansa.
708091