Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ta hada shi da daya daga cikin fitattun makaranta na duniyar musulmi Ridwan Darwsish daga kasar Syria ya bayyana cewa, sa ido da kyakkyawar kula daga mambobin kwamitin alkalan gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki na da matukar muhmmanci a cikin harkokin gasar kur'ani mai tsarki.
Ya ci gaba da cewa alkur'ani mai tsarki ya kebantu da wasu abubuwa da babu wani abu ko wani littafi da ya kebantu da su, saboda haka gudanar da gasa a bangaren karatunsa ko sanin ka'idojin karatunsa, ko sanin wasu ilmomi da ke cikinsa lamari ne mai girma da ke bukatar sa hankali.
Ya ce a masaniyar da yake da ita ta halartar tarukan gasar kur'ani mai tsarki a sassa daban-daban na duniya, ya fahimci cewa kula da sa ido a lokacin alkalanci suna daga cikin muhimman abubuwa.
709113