Bangaren kasa da kasa, Za a gudanar da wani zama da aka baiwa taken addinin muslunci a cikin kasar faransa da kuma raya addini, da nufin tattauna muhimman batutuwa da suka danganci matsayin addinin muslunci a halin yanzu a cikin kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar na mosque-Lyon an bayyana cewa, za a gudanar da wani zama da aka baiwa taken addinin muslunci a cikin kasar faransa da kuma raya addini, da nufin tattauna muhimman batutuwa da suka danganci matsayin addinin muslunci a halin yanzu a cikin kasar ta Faransa.
Wannan zaman taro dai za a gudanar da shi a birnin Lyon, wanda zai samu halartar masana daga sassa daba-daban na kasar, da suka hada da malaman jami'a gami da malaman addini na muslunci da ma malaman addinin kirista.
Dukkanin bangarorin za su bijiro da iyakacin fahimtarsu dangane da ci gaban addinin muslunci da kuma matsayinsa kan lamurra da dama da suka danganci rayuwar dan adam ta zamantakewa, musamamn ma a wannan zamani.
709252