Bangaren kasa da kasa, jami'an lardin Karbala sun bayyana cewa sun kammala dukkanin shirye-shirye a birnin mai alfarma domin tarbar bakin Imam Hussain (AS) da za su halarci tarukan Ashura a wannan shekara.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na alkauthar na yanar gizo cewa, jami'an lardin Karbala sun bayyana cewa sun kammala dukkanin shirye-shirye a birnin mai alfarma domin tarbar bakin Imam Hussain (AS) da za su halarci tarukan Ashura a wannan shekara da muke ciki.
Bayanin ya ce kamar yadda aka saba a kowace shekara, akan gudanar da dukkanin shirye-shiryen da suka kamata domin tarbar miliyoyin baki da za su halarci tarukan Ashura a birnin Karbala mai alfarma a hubbaren Imam Hussain (AS) da kuma hubbaren Abul fadl Abbas (AS) da ke birnin.
A nasu bangaren kuma jami'an tsaro tuni suka sanar cewa sun kammala daukar dukkanin matakan da suka dace domin bayar da kariya ga masu ziyara, da kuma tabbatar da tsaro a lokacin gudanar da tarukan.
709246