Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta Nunu ya watsa rahoton cewa; komandan yan sandan birnin Najaf mai tsarki sun karya ta labarin da wata kafar labarai ta tauraron dan adam ke yadawa kan kokarin makircin aikata kisan gilla na ta'addancin kan ayatullahi Uzma Said Sistani babban marji'in addini nay an shi'a a kasar Iraki.Tuni jami'an tsaro suka dauki matakan tsaro da tsauraren daukan matakan tsaron a gurare masu daraja kamar hubbarin imam Ali (AS) da gidajen maraji'ai da gurare masu tsarki kuma ba a barin kowa ne ya riki makami a kusa da inguwar da Ayatullahi Sistani ke zaune.
709867