IQNA

Mohammad Javad Gohari Zai Gabatar Da Tarjamarsa Ta Ga Iqna

10:16 - December 14, 2010
Lambar Labari: 2047756
Bangaren kasa da kasa Muhammad Jawad Gohari malamin jami'ar Oxford ta kasar Birtaniya ya sanar cewa zai gabatar wa kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna tarjamar alkur'ani mai tsarki da ya yi a ranar Talata.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga bangaren yada labaransa akasar Birtaniya an habarta cewa, muhammad Jawad Gohari malamin jami'ar Oxford ta kasar Birtaniya ya sanar cewa zai gabatar wa kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna tarjamar alkur'ani mai tsarki da ya yi a ranar yau.

Ya ci gaba da cewa aikin da ya gudanar na tarjamar kur'ani mai tsarki aiki mai matukar muhimmanci a wurinsa, domin kuwa ta wannan hanyar zai iya isar da sakon addininsa ga sauran mutanen da suke fahimtar turancin Ingilishi, ta yadda za su iya karanta kur'ani mai tsarki kuma su fahimci ma'anoninsa.

Wannan rahoto ya yi nuni da cewa Muhammad Jawad Gohari malamin jami'ar Oxford ta kasar Birtaniya ya sanar cewa zai gabatar wa kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna tarjamar alkur'ani mai tsarki da ya yi a ranar yau Talata da muke ciki.

712202



captcha