IQNA

Taro Kan Sulhu,Hadin Kai Da Daidaito A Mahangar Musulunci

14:26 - December 14, 2010
Lambar Labari: 2048014
Bangaren kasa da kasa; a ranar ashirin da daya ga watan azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a garin Lakhunu da ke lardin Utar Paradesh na kasar Indiya aka gudanar da taro kan sulhu,hadin kai da daidaito a mahangar kur'ani mai girma.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta Two Circles ya watsa rahoton cewa; a ranar ashirin da daya ga watan azar na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a garin Lakhunu da ke lardin Utar Paradesh na kasar Indiya aka gudanar da taro kan sulhu,hadin kai da daidaito a mahangar kur'ani mai girma.Laxmishankra Acharya wani fitattace dan gwagwarmaya a harkokin da suka shafi zamantakewa a cikin jawabin day a gabatar a lokacin gudanar da wannan taro ya bayyana cewa; musulminci addini ne na tabbatar da sulhu hadin kai da daidaito a tsakanin yan adam ta fuskar zamantakewa amma idan wani bai fahimci hakikanin addinin Musulunci bad a ma'anonin kur'ani mai girma to zai siffata wannan addini da siffo da suak sha bamban da shi .


711701

captcha