Bangaren kasa da kasa;kungiyar da ke fada da nuna wariyar launin fata da na addini da kuma ke kokarin samar da jituwa da fahimtar juna karakashin abuktaka a tsakanin al'umma ta Mrap da ke kasar Faransa a ranar ashirin da daya ga watan azar na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya ta aikewa da magajin garin birnin Paris da wata wasika da a cikinta suka bukaci a hana gudanar da taron kasa da kasa kan Musulunci da musulmi da kuma yin Allah wadai.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne bayan ya nakalto daga majiyar labarai ta donnetonavis ya watsa rahoton cewa; kungiyar da ke fada da nuna wariyar launin fata da na addini da kuma ke kokarin samar da jituwa da fahimtar juna karakashin abuktaka a tsakanin al'umma ta Mrap da ke kasar Faransa a ranar ashirin da daya ga watan azar na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya ta aikewa da magajin garin birnin Paris da wata wasika da a cikinta suka bukaci a hana gudanar da taron kasa da kasa kan Musulunci da musulmi da kuma yin Allah wadai. A cikin wannan doguwar wasika sun yi bayani dalla-dalla kan manufar wannan taro da abubuwan da zai iya biyo bayan da kuma wadanda suka biyo bayan irin jawabai da magangani da ingiza jama'a da masu manufofi na wariya suka haddasa a tsakanin jama'a da kuma haddasa rikici a tsakanin al'ummar kasar.
711708