IQNA

Wasu 'Yan Siyasa Na Yin Kamfe Da Kyamar Musulunci A Faransa

12:58 - December 18, 2010
Lambar Labari: 2048967
Bangaren kasa da kasa, Wasu fitattun 'yan siyasa a kasar Faransa suna kamfen neman kuri'a ta hanayar nuna kyama ga addinin muslunci tare da danganta musulunci da ayyukan ta'addanci.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na fr.zaman an bayyan acewa, wasu fitattun 'yan siyasa a kasar Faransa suna kamfen neman kuri'a ta hanayar nuna kyama ga addinin muslunci a fadin kasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa daga cikin irin wadannan siyasa kuwa har da wadanada suka samu kuri'a da dama daga musulmi wajen darewa kan mukamai a cikin gwamnatin kasarta Faransa, wanda kuma goyon bayan da musulmi suka nuna musu ya yi tasiri a cikin harkar siyasarsu.

Kasar Faransa dai na daya daga cikin kasashen turai da suke da yawan musulmi, inda daga bisani aka samu wasu masu tsananin kyamar addinin muslunci suka fara daukar matakan nuna wariya da kyma ga mabiya addinin Musulunci.

A kwanakin baya mataimakin shugaban jam'iyya mai mulki a kasar Faransa ya yi wani dangane da addinin muslunci, inda da dama daga cikin musulmin kasar har m da kiristoci da yahudawa suka nuna rashin gamsuwarsu.

713295
captcha