Bangaren kasa da kasa, An gudanar da taron bude masallaci mafi girma a dukkanin yankin turai ta yamma a birnin Roterdam na kasar Holland, wanda zai zama babban wurin gudanar da tarukan addinin muslunci a birnin da ma sauran sassa kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na eroupe na yanar gizo an bayyana cewa, an gudanar da taron bude masallaci mafi girma a dukkanin yankin turai ta yamma a birnin Roterdam na kasar Holland da ke yammacin nahiyar turai.
Taron bude masalalcin ya samu halartar wasu daga cikin wailan kungiyoyin farar hula na kasar, gami da malaman jami'a da kuma wakilai na kungiyoyin musulmi da suke garuruwa daban-daban na kasar, kuma hakan ya kawatar da wasu daga cikin mutanen kasar.
Gina masallacin ya dauki shekaru kimanin bakwai wanda aka fara daga shekara ta 2003, sakamakon matsalolin da aka yi ta fuskanta daga masu tsatsauran ra'ayin kyamar Musulunci, ginin ya samu tsaiko.
713614