IQNA

Makiya Na Son Cimma Manufarsu Ta Hanyar Haddasa Fitinar Addini

10:16 - December 19, 2010
Lambar Labari: 2049481
Bangaren siyasa da zamantakewa: kungiyar malamai musulmi a kasar Labanon a ranar ashirin da shidda ga watan azar na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a wani zama da suka gudanar a birnin Bairut fadar mulkin wannan kasa makiya kamar su harammatacciyar kasar Isra'ila da masu manufa ta sahayoniya na son cimma manufarsu ce ta hanyar haddasa fitina ta mazhaba a tsakanin musulmi.

Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; kungiyar malamai musulmi a kasar Labanon a ranar ashirin da shidda ga watan azar na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya a wani zama da suka gudanar a birnin Bairut fadar mulkin wannan kasa makiya kamar su harammatacciyar kasar Isra'ila da masu manufa ta sahayoniya na son cimma manufarsu ce ta hanyar haddasa fitina ta mazhaba a tsakanin musulmi. Wannan kungiyar ta malaman addinin Musulunci a kasar ta labanon ta jaddada cewa; duk wani makirci da kokarin haddasa fitina a tsakanin musulmi wani bata lokaci ne kuma da yardar Allah Madaukakin sarki ba za su cimma nasara ba kuma za mayar masu da aniyarsu ko shakka babu domin kan musulmi ya waye.


713836
captcha