IQNA

Za A Fara Gudanar Da Gasar Kur'ani Ta Kasa Kasa A Kasar Saudiyya

15:46 - December 26, 2010
Lambar Labari: 2053610
Bangaren kasa da kasa, Za a fara gudanar da gasar karatun kur'ani a matsayi na duniya a kasar Saudiyya gobe idan Allah ya kaimu, tare da halartar makaranta da mahardata kur'ani mai tsaki daga sassa daban-daban na duniya.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar iqtisadiyya da ake bugawa a kasar Saudiyya an habarta cewa za a fara gudanar da gasar karatun kur'ani a matsayi na duniya a kasar Saudiyya gobe idan Allah ya kaimu, tare da halartar makaranta da mahardata kur'ani mai tsaki daga sassa daban-daban na duniya musamman daga kasashen musulmi.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan ma'aikatar kula da ayyukan musulunci ta kasar Saudiyya ita ce ta dauki nauyin gudanar da wannan gasar karatu da hardar kur'ani, tare da hadin gwiwa da kwamitocin gasar kur'ani na kasashe.

Za a fara gudanar da gasar karatun kur'ani a matsayi na duniya a kasar Saudiyya gobe idan Allah ya kaimu, tare da halartar makaranta da mahardata kur'ani mai tsaki daga sassa daban-daban na duniya da kuma na larabawa.

717617




captcha