Bangaren kasa da kasa, An yi kira ga dukkanin bangarorin palastinawa kama daga na siyasa har zuwa na gwagwarmaya da su hada kai domin fuskantar zalunci da mamayar yahudawan sahyuniya a cikin yankunan palastinawa da suke ci gaba da mamayewa.
Kamafanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga majiyar labarai na kasar Sana ne ya watsa rahoton cewa: kasuwar baje kolin zama daya tsintsiya guda tare da al'ummar Gaza da zummar nuna bakin cikin kan wuce gonad a irin haramtacciyar kasar Isra'ila yar mamaye kan al'ummar Palasdinu da ofishin al'adu na garin halb ya shirya.
Gudanar da irin wannan taro ko shakka babu zai taimaka matuka gaya wajen hadin kai a tsakanin musulmi da larabawa da kuma ci gaba da nuna damuwa da halin kunci da al'ummar Gaza suke ciki karkashin zalunci da wuce gonad a irin harammatcciyar kasar Isra'ila yan mamaya.
Da dama daga cikin masana kan harkokin yankin gabas ta tsakiya dai suna dora alhakin rashin samun hadin kai tsaknain palastinawa mazauna yankin gabar yamma da kogin Jordan da kuma sauran yankunan zirin Gaza kan mahukuntan Ramallah.
721516