IQNA

Za A Gudanar Da Zaman Taro Kan Koyarwar Manzon Allah (SAW) A faransa

11:22 - January 04, 2011
Lambar Labari: 2058623
Bangaren kasa da kasa, Za a gudanar da wani zaman taro a birnin Lyon na kasar Faransa da zai yi dubi kan matsayin koyarwar manzon Allah (SAW) da kuma muhimmancin yin aiki da ita a cikin rayuwa ta musulmi, da tasirinta a cikin rayuwar zamantakewar jama'a baki daya.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga wani shafin sadarwa na yanar gizo na ujm cewa, za a gudanar da wani zaman taro a birnin Lyon na kasar Faransa da zai yi dubi kan matsayin koyarwar manzon Allah (SAW) da kuma muhimmancin yin aiki da ita a cikin rayuwa ta musulmi, da tasirinta a cikin rayuwar zamantakewar jama'a baki daya, tsakanin musulmi da ma wadanda ba musulmi ba.

Babbar cibiyar kula da ayyukan muslunci ta birnin Lyon ce ta dauki nauyin shiryawa da kuma gudanar da wannan zaman taro, wanda zai samu halartar masana daga sassa daban-daban na kasar farnsa da kewaye.

Babban sakataren cibiyar ya bayayna cewa manufar gudanar da wannan zaman taro dai tana da dangantaka ne kai tsaye da muhimmancin koyarwar manzon Allah ga musulmi da ked a imani sa dakon manzo.

723363




captcha