IQNA

An Girmama Wadanda Suka Gudanar Da Gasar Kur'ani Ta Duniya A Saudiyya

11:23 - January 04, 2011
Lambar Labari: 2058625
Bangaren kasa da kasa, An girmama makaranta da mahardata kur'ani mai tsarki da suka halarci gasar karatu da harda da aka gudanar a kasar Saudiyya a matsayi na kasa da kasa, da nufin karfafa gwiwarsu da kuma kwadaitar da sauran matasa masu bukatar shiga harkokin gasar kur'ani.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar kasar Saudiyya an habarta cewa, an girmama makaranta da mahardata kur'ani mai tsarki da suka halarci gasar karatu da harda da aka gudanar a kasar Saudiyya a matsayi na kasa da kasa, da nufin karfafa gwiwarsu da kuma kwadaitar da sauran matasa masu bukatar shiga harkokin gasar kur'ani mai tsarki.

Yanzu haka dai dukkanin wadanda suka shiga cikin gasar sun sheda karamcin da aka nuna musu a lokacin da suke karbar kyautuka daga jami'an ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar saudiyya da kuma wasu daga cikin masu shirya gasa a kasar a matsayi na kasa.

Da dama daga cikin masu shiga gasar karatun kur'ani mai tsarki suna halartar cibiyoyi na musamman ne domin samun cikakken horo kan harda da kuma karatu, ta yadda zasu samu cikakken shiri kafin shiga gasa.

723325






captcha