Bangaren kasa da kasa, Babban malamin jami'ar Azhar da ke birnin Alkahira na kasar masar Sheikh Ahmad Tayyib ya bayyana cewa, shigar kasashen ketare na yammacin turai a cikin harkokin yankin gabas ta tsakiya shi ne babbar barazana ga yankin ba yaduwar shi'a ba.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-jiwar cewa, babban malamin jami'ar Azhar da ke birnin Alkahira na kasar masar Sheikh Ahmad Tayyib ya bayyana cewa, shigar kasashen ketare na yammacin turai a cikin harkokin yankin gabas ta tsakiya shi ne babbar barazana ga yankin ba yaduwar shi'a ba kamar yadda wasu suke rayawa.
Babban malamin Azhar din ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a birnin Alkahira, ya ci gaba da cewa jamia'ar Azhar bat a da wata dangataka da siyasa a matsayinta na babbar cibiyar ilimi ta kasar.
Ya sheda hakan ne alokacin da aka tambaye shi kan matsayinsa da kuma jami'ar Azhar dangane da zaben da aka gudanar a kasar, da kuma yadda aka mayar da kungiyar Ikhwanul muslimin saniyar ware.
723140