Bangaren kasa da kasa, An fara gudanar da wani taro na baje koli kan kayyaki da suka hada da hotuna kan yanayin da Palastinawa suke ciki na wahala, sakamakon zalunci da danniyar da haramtacciyar kasar Isra'ila a kansu.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a wani rahoto day a nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dillancin labaran SANA na kasar Syria cewa, an fara gudanar da wani taro na baje koli kan kayyaki da suka hada da hotuna kan yanayin da Palastinawa suke ciki na wahala, sakamakon zalunci da danniyar da haramtacciyar kasar Isra'ila a kansu na tsawon shekaru.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan baje koli ya hada da nuna wasu hotuna na daruruwan palastinawa da suka yi shahada tun tsawon shekaru da yankin nasu ya kasance karkashin mamamyar haramtacciyar kasar, da kuma yadda sojojin yahudawan sahyuniya suke yin amfani da karfin soji a kan palastinawa fararen hula.
Fara gudanar da wani taro na baje koli kan kayyaki da suka hada da hotuna kan yanayin da Palastinawa suke ciki na wahala, sakamakon zalunci da danniyar da haramtacciyar kasar Isra'ila a kansu, babban ci gaba ne ta fuskacin fadakar al'ummomin duniya dangane da halin da ake ciki a Palastinu.
730544