IQNA

Kamracin Malaman Kur'ani Na Daga Cikin Manyan Matsalolin Makarantun Indonesia

13:59 - January 17, 2011
Lambar Labari: 2066143
Bangaren kasa da kasa, Karancin malaman kur'ani gogaggu na daga cikin manyan matsaloli da makarantun kasar Indonesia ke fuskanta a cikin wannan lokaci, bisa la'akari da karuwar dalibai masu sha'awar koyon karatun kur'ani mai tsarki a kasar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Aljazeera net an bayyana cewa, matsalar karancin malaman kur'ani gogaggu na daga cikin manyan matsaloli da makarantun kasar Indonesia ke fuskanta a cikin wannan lokaci, bisa la'akari da karuwar dalibai masu sha'awar koyon karatun kur'ani mai tsarki a kasar ta Indonesia.

Rahoton ya ce matasalar tafi yin kamari a makarantun da ake koyar da makafi, domin kuuwa suna bukatar malamai da suke da masaniya kan hanyoyi na musamman da za a iya koyar da wanda ba ya gani, bugu da kari kuma akwai matsaloli samar da kayayyakin da ake yin amfani da su a wannan bangare.

Matsala karancin malaman kur'ani gogaggu na daga cikin manyan matsaloli da makarantun kasar Indonesia ke fuskanta a cikin wannan lokaci, bisa la'akari da karuwar dalibai masu sha'awar koyon karatun kur'ani mai tsarki a kasar da ta fi yawan musulmi a duniya.

731058



captcha