IQNA

An dakatar Da Tattaunawa Tsakanin Azhar Da Fadar Vatican

20:00 - January 22, 2011
Lambar Labari: 2068776
Bangaren kasa da kasa, An dakatar da tattaunawar da aka fara gudanarwa tsakanin babbar jami’ar musulunci ta Azhar da ke birnin Alkahira fadar mulkin kasar Masar da kuma fadar Vatican ta mabiya addnin kirista.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Azhar an bayyana cewa, an dakatar da tattaunawar da aka fara gudanarwa tsakanin babbar jami’ar musulunci ta Azhar da ke birnin Alkahira fadar mulkin kasar Masar da kuma fadar Vatican ta mabiya addnin kirista dake kasar Italia, wadda aka fa tun lokutan baya.
Babban malamin jami’ar Azhar Ahmad Tayyib ya fitar da wani bayani da a cikins aya bayyana cewa, babban dalilin dakatar da wannan tattaunawa tsakanin Azhar da kuma fadar Vatican, shi ne yadda paparoma na 16 ya sake maimata cin fuska ga addinin addinin muslunci, wanda hakan ya yi hannun riga da manufofin tattaunawar.
Dakatar da tattaunawar da aka fara gudanarwa tsakanin babbar jami’ar musulunci ta Azhar da ke birnin Alkahira fadar mulkin kasar Masar da kuma fadar Vatican ta mabiya addnin kirista, wani baban sako ne ga paparoma kan rashin lissafinsa, da kuma bin son rai kan yadda yake kokarin bayyana ma mabiyansa addinin musulunci.
734212


captcha