IQNA

Jami'ar Azhar Ta Ki Amincewa Da Takardun Shedar Cibiyar Kur'ani Ta Kuwait

15:04 - January 24, 2011
Lambar Labari: 2069521
Bangaren kasa da kasa, Babban darakatan cibiyar nazari da bincike ta ilmomin Musulunci ta kasar Kuwait da ke karkashin ma'aikatar kula da ayyukan addini ta kasar, ya bayyana cewa jami'ar Azhar taki amincewa da takardun shedar kammala karatu a cibiyar.



Kamfanin dillancin labaran kur'ani mai tsarki na iqna ya nakalto rahoto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar al-qabs ta kasar Kuwait cewa, babban darakatan cibiyar nazari da bincike ta ilmomin Musulunci ta kasar Kuwait da ke karkashin ma'aikatar kula da ayyukan addini ta kasar, ya bayyana cewa jami'ar Azhar taki amincewa da takardun shedar kammala karatu a cibiyar da wasu masu nazari suka nemi shiga Azhar da su.

Ya ce dukkanin darussan da jami'ar Azhar ke bukata wannan jami'a tana koyar da su, kuma dukkanin wadanda suka nemi shiga jami'ar Azhar din sun karanta darussan da ake bukata, a kan haka y ace bai san dalilin daukar wannan mataki daga jami'ar da ake kallonta amatsayin babbar jami'ar Musulunci ta duniya ba.

Darakatan cibiyar nazari da bincike ta ilmomin Musulunci ta kasar Kuwait da ke karkashin ma'aikatar kula da ayyukan addini ta kasar, ya bayyana cewa jami'ar Azhar taki amincewa da takardun shedar kammala karatu a cibiyar, ya nuna matukar rashin jin dadinsa kan daukar wannan mataki daga Azhar.

735154

captcha