IQNA

Ayyukan Hadin Gwiwa Tsakanin Cibiyar Ilimi Ta Qom Da Jami'ar Postdam

12:18 - February 15, 2011
Lambar Labari: 2081292
Bangaren kasa da kasa, Cibiyar ilimi ta birnin Qom ta cimma matasaya tsakaninta da kuma jami'ar birnin Postdam na kasar Jamus dangane da batun kara bunkasa harkokin ilimi na addini da tarihi da kuma falsafa, gami da sauran ilmomin da suka yi gamayya a cikinsu.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na karamin ofishin jakadancin jamhuriyar Musulunci ta ran da ke kasar jamus an bayyana cewa, cibiyar ilimi ta birnin Qom ta cimma matasaya tsakaninta da kuma jami'ar birnin Postdam na kasar Jamus dangane da batun kara bunkasa harkokin ilimi na addini da tarihi da kuma falsafa, gami da sauran ilmomin da suka yi gamayya a kai.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shirin za a fara aiwatar da shi ne a cikin shekara ta shamsiyya mai kamawa, inda jami'ai da wakilai daga dukkanin bangarorin biyu za su hadu domin tattaunawa da juna, da kuma samun matasaya guda daya kan dukkanin abubuwan da suka amince da su tare da rattaba hannu.

Cibiyar ilimi ta birnin Qom ta cimma matasaya tsakaninta da kuma jami'ar birnin Postdam na kasar Jamus dangane da batun kara bunkasa harkokin ilimi na addini da tarihi da kuma falsafa, gami da sauran ilmomin da suka yi gamayya a cikinsu.

747549


captcha