Bangaren kasa da kasa, An fara gudanar da wani taro da ke yin dubi dangane da matsayin manzon Allah (SAW) da kuma dabiunsa da sakonsa zuwa ga talikai, wanda ake gudanarwa a kasar Iraki a daidai lokacin gudanar da taruka na tunawa da lokacin haihuwarsa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na alkausar cewa, an fara gudanar da wani taro da ke yin dubi dangane da matsayin manzon Allah (SAW) da kuma dabiunsa da sakonsa zuwa ga talikai, wanda ake gudanarwa a kasar Iraki a daidai lokacin gudanar da taruka na tunawa da lokacin haihuwarsa a ko'ina cikin fadin duniya.
Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haka ana ci gaba da gudanar da zaman taron a birnin Kofa, tare da halartar wakilan manyan malaman addinin muslunci na birnin Najaf da ake komawa zuwa gare su, da kuma malaman 'yan sunna da wakilan cibiyoyin ilimi daban-daban na kasar Iraki da wasu daga cikin kasashen musulmi da na larabawa.
Manzon Allah (SAW) yana dauke da sakon haske ne ga dukkanin 'yan adam daga Allah madaukakin sarki, domin shiryar da su zuwa ga abin da mahaliccinsu ya halicce su don shi, a kan haka ne zaman taron ya mayar da hankali kan ayar da ke tabbatar da cewa manzon yana kan kyawawan dabi'u.
An fara gudanar da wani taro da ke yin dubi dangane da matsayin manzon Allah (SAW) da kuma dabiunsa da sakonsa zuwa ga talikai, wanda ake gudanarwa a kasar Iraki a daidai lokacin gudanar da taruka na tunawa da lokacin haihuwarsa.
750854