IQNA

Za A Gudanar Da Zaman Taron Musulmin Kasar Faransa Na Shekara-Shekara

15:09 - March 01, 2011
Lambar Labari: 2088590
Bangaren kasa da kasa, Za a fara gudanar da zaman taron mabiya addinin muslunci na kasar faransa a karo na ashirin da shida a cikin watan gobe, wanda za a gudanar a babban dakin taruka na baje kolin Borje da ke cikin birin Paris.


Kamfanin diallancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo Oumma an bayyana cewa, za a fara gudanar da zaman taron mabiya addinin muslunci na kasar faransa a karo na ashirin da shida a cikin watan gobe, wanda za a gudanar a babban dakin taruka na baje kolin Borje da ke cikin birin Paris fadar mulkin kasar faransa.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zaman taron yana da matukar muhimmanci ga mabiy addinin Musulunci na kasar faransa, inda a nan suke tattauna dukkanin muhimman batutuwa da suka shafi harkokin muslunci da musulmin kasar baki daya, da kuma daukar matakai na bunkasa harkokin addininsu.

Za a fara gudanar da zaman taron mabiya addinin muslunci na kasar faransa a karo na ashirin da shida a cikin watan gobe, wanda za a gudanar a babban dakin taruka na baje kolin Borje da ke cikin birin Paris na kasar.

754805


captcha