Bangaren kasa da kasa, Za a gudanar da gasar karatun kur’ani mai tsarki da hadisin manzon Allah (SAW) a birnin Riyad fadar mulkin kasar Saudiyya, wanda za a fara gudanarwa a cikin mako mai kamawa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Nasij an bayyana cewa, za a gudanar da gasar karatun kur’ani mai tsarki da hadisin manzon Allah (SAW) a birnin Riyad fadar mulkin kasar Saudiyya, wanda za a fara gudanarwa a cikin mako mai kamawa babban ginin gudanar da taruka da ke tsakiyar birnin.
Shugaban hukumar kula da ayyukan gasar karatun kur’ani ta kasa Ahmad Bu Ali ya bayyana cewa, babbar manufar gudanar da wannan gasar ita ce samar da wani yanayi na karfafa gwiwar matasa ta fuskar mayar da hankali kan koyarwar kur’ani da hadisan ma’aiki, wanda hakan zai ba su damar sanin addini tun daga kuruciyarsu.
Gudanar da gasar karatun kur’ani mai tsarki da hadisin manzon Allah (SAW) a birnin Riyad fadar mulkin kasar Saudiyya, wanda za a fara gudanarwa a cikin mako mai kamawa, zai zo a karo na shida da ake gudanar da irinta a kasar.
756647