IQNA

Malaman Makarantun Kur'ani A Birnin Karbala Sun Gudanar Da Zama

18:14 - March 07, 2011
Lambar Labari: 2092000
Bangaren kasa da kasa, malaman kur'ani a makarantu da cibiyoyin kur'ani mai tsarki a birnin karbala sun gudanar da zamansu a babban dakin gudanar da taruka na birnin da ke cikin harabar hubbaren Imam Hussain (AS) mai tsarki.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Muzn an bayyana cewa, malaman kur'ani a makarantu da cibiyoyin kur'ani mai tsarki a birnin karbala sun gudanar da zamansu a babban dakin gudanar da taruka na birnin da ke cikin harabar hubbaren Imam Hussain (AS) mai tsarki inda a akan gudanar da taruka na addini.

Bayanin ya ci gaba da cewa babbar manufar gudanar da zaman taron na yau ita tattauna muhimman batutuwa da suka danganci harkokin koyarwa da kuma yadda za a kara bunkasa lamurran kur'ani mai tsarki a cikin rayuwar zamantakewa ta a'ummar musulmin kasar Iraki, ta yadda za a ga tasirin koyawar addinin Musulunci a rayuwar jama'a.

Malaman kur'ani a makarantu da cibiyoyin kur'ani mai tsarki a birnin karbala sun gudanar da zamansu a babban dakin gudanar da taruka na birnin da ke cikin harabar hubbaren Imam Hussain (AS) mai tsarki.

758693




captcha