Bangaren kasa da kasa, Tun bayan harin goma sha daya ga watan satumba wasu suka shiga yada kiyayya da gaba kan addinin musulunci a cikin kasashen yammacin turai da nufin buce haskensa, lamarin da ya kara yada shi a cikin wadannan kasashe fiye da sauran lokutan da suka gabata.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ta hada shi da daya daga cikin masana na kasar Jamus Muhannid Khorshid ya bayyana cewa, tun bayan harin goma sha daya ga watan satumba wasu suka shiga yada kiyayya da gaba kan addinin musulunci a cikin kasashen yammacin turai da nufin buce haskensa, lamarin da ya kara yada shi a cikin wadannan kasashe fiye da sauran lokutan da suka gabata a cikin tarihi.
Masanin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake halaratar taron kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da ake gudanrwa a duk shekara, wanda a halin yanzu ake gudanarwa akaro na ashirin da hudu, inda ya ce hakikanin gaskiya reshe ya juye da mujiya, domin kuwa harin satumba an yi nufin bakanta surar musulunci da shi, amma sai lamarin ya zama sabanin hakan.
Tun bayan harin goma sha daya ga watan satumba wasu suka shiga yada kiyayya da gaba kan addinin musulunci a cikin kasashen yammacin turai da nufin buce haskensa, lamarin da ya kara yada shi a cikin wadannan kasashe fiye da sauran lokutan da suka gabata.
758584