Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto aga shafin sadarwa na yanar gizo na OIC cewa, Kungiyar kasashen musulmi ta OIC za ta gudanar da wani zama na musamman kan rikicin da ke faruwa akasar Libya, da kuma yanayin da dubban daruruwan mutane 'yan gudun hijira suke ciki a kasar da kuma kan iyakokinta da sauran makwabta.
Inda har yanzu haka a ksar ta Libya ake ci gaba da fafatawa tsakanin masu neman sauyi da kuma sojoji masu biyayya da shugaban Libya Mu'ammar Gaddafi a sassa daban-daban na kasar, inda a cikin makon nan ne gidan talabijin din gwamnatin Libya da Gaddafi ke iko da shi ya sanar da kame garin Zawiyya, bayan masu fafutuka sun kwace shi daga ikon Gaddafi.
Daga bisani masu fafutukar sun tabbatar da cewa sun sake fatattakar sojojin Gaddafi, bayan wani gumurzu mai tsanani, lamarin da ya yi sanadiyar rasa rayuan mutane da dama daga bangarorin biyu.
A bangare guda kuma majalisar kasa ta wucin gadi a kasar Libya ta nuna rashin amincewarta dangane da duk wani shishigi da sojojin ketare ka iya yi a cikin kasar ta Libya.
Masu bore a kasar ta Libya sun sallami wasu jami'an tsaron kasar Britania 8 wadanda suka kama a ranar juma'ar da ta gabata a cikin kasar suna dauke da kayakin aiki na aikewa da sakonni daga nesa.
758955