IQNA

Za A Gudanar Da Gazasar Zabar Masallaci Mafi Kyau A Kasar Holland

20:41 - March 12, 2011
Lambar Labari: 2094466
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da gasar zabar masallaci mafi kyau a tsakanin masallatan kasar Holland, da nufin kara fiito da matsayin al’adu da kuma yanayin zamantakewar rayuwa ta musulmi mazauna kasar.
Kamfanin dillancin labaraniqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na muhit an bayyana cewa, za a gudanar da gasar zabar masallaci mafi kyau a tsakanin masallatan kasar Holland, da nufin kara fiito da matsayin al’adu da kuma yanayin zamantakewar rayuwa ta musulmi mazauna kasar ta Holland.
Yanzu haka dai mabiya addnin muslunci na kasar sun shirya kafa wani kwamiti da zai hada da malaman masallatai da kuma masana musulmi daga sassa daban-daban na kasar, wanda zai dauki nauyin shiryawa da kuma gudanar da wannan gasa, inda za a sanar da sunayen masallatan da gasar za ta hada su.
za a gudanar da gasar zabar masallaci mafi kyau a tsakanin masallatan kasar Holland, da nufin kara fiito da matsayin al’adu da kuma yanayin zamantakewar rayuwa ta musulmi mazauna kasar.
761552


captcha