IQNA

Kasashe 46 Ne Ke Halartar Gasar Kur’ani Ta Kasa Da Kasa A Birnin Doha Na Qatar

12:42 - March 13, 2011
Lambar Labari: 2094712
Bangaren kasa da kasa, Sama da kasashe arba’in shida ne halatar gasar karatun kur’ani mai tsarki da ta kebanci kanan yara a birnin Doha na kasar Qatar, wadda ake gudanarrwa a mataki na kasa da kasa, kamar yadda cibiyar kula da shirya taruka na kur’ani a kasar ta bayyana.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na islam online an bayyana cewa, Sama da kasashe arba’in shida ne halatar gasar karatun kur’ani mai tsarki da ta kebanci kanan yara a birnin Doha na kasar Qatar, wadda ake gudanarrwa a mataki na kasa da kasa, kamar yadda cibiyar kula da shirya taruka na kur’ani a kasar ta bayyana ga kafofin yada labarai na kasar da ma na ketare.
Bayanin ya ci gaba da cewa, wannan gasa an shirya ta ne bisa hadin gwiwa tsakanin hukumar kula da harkokin addini ta kasar katar da kuma babbar cibiyar kula da harkokin kur’ani mai tsarki gami tashar talabijin din aljazeera ta yara da ke watsa shirye-shiryenta kan tauraron dan adam.
Sama da kasashe arba’in shida ne halatar gasar karatun kur’ani mai tsarki da ta kebanci kanan yara a birnin Doha na kasar Qatar, wadda ake gudanarrwa a mataki na kasa da kasa, kamar yadda cibiyar kula da shirya taruka na kur’ani a kasar ta bayyana.
762104
captcha