Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na rasid an bayyana cewa, malaman mabiya mazhabar shi'a akasar Saudiyya sun bukaci mahukuntan kasar da su gudanar da sauye-sauye a cikin harkokin siyasa da mulkin kasar, haka nan kuma sun yi Allawadai da harbin masu zanga-zangar lumana da jami'an tsaron kasar suka yi a Katif da Ihsa da ke gabacin kasar.
A wani mataki na yunkurin murkushe zanga-zangar lumana da al'ummar kasar Bahrain ke gudanarwa domin neman hakkokinsu na siyasa a matsayinsu na 'yan kasa, gidan sarautar Bahrain a yammacin jiya tare da hadin baki da gwamnatin Saudiyya ya aike da sojoji cikin shirin yaki zuwa kasar ta Bahrain.
Wata majiyar tsaro a kasar Saudiyya ta fadi cewa, mahukuntan Saudiyya sun aike da sojoji sama da dubu daya zuwa kasar Bahrain ne domin murkushe zanga-zangar da ake gudanarwa a fadin kasar, domin neman gudanar da sauye-sauye a cikin sha'anin mulkin kasar.
Tun bayan da al'ummar kasar Bahrain suka fara gudanar da zanga-zangar lumana a ranar 14 ga watan Fabrairun da ya gabata, jami'an tsaron kasar ta Bahrain, da suka hada da soji gami da 'yan sanda, wadanda akasarinsu ba 'yan asalin kasar ba ne, sun afka kan fararen hular da suke gudanar da zangar-zangar, inda suka kashe wasu ta hanyar harbi da harsasan bindiga, tare da jikkata wasu daruruwa.
Kasashen duniya da dama sun yi Allawadai da gidan sarautar Bahrain, wanda turawan birtaniya suka kafa, lamarin da ga alama ya yi tasiri wajen sa mahukutan na Bahrain suka janye soji daga kan tituna, kuma suka gudanar da 'yan sauye-sauye a cikin wasu ma'aikatun kasar, amma hakan ko alama bai gamsar da al'ummar kasar da suke neman sauyi na hakika ba.
A cikin shekara ta 2001, mahukuntan Bahrain sun kirayi bangarorin adawa zuwa ga tattaunawa, amma har inda yau take ba su aiwatar da ko daya daga cikin abubuwan da aka amince da su zaman tattaunawar ba, lamarin da ya sanya al'ummar kasar a halin yanzu suke kallon alkawullan da mahukuntan suke yi a matsayin wani sabon salo na yaudara.
763407