Bangaren kasa da kasa, ana shirin gudanar da taron kasa da kasa kan harkokin abinci da kayan halal a birnin Kualalampour fadar mulkin kasar Malazia a karo na shida, tare da halartar masana daga sassa daban-daban na kasashen musulmi da na larabawa da kuma na yankin Asia.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Halal Focus an habarta cewa, ana shirin gudanar da taron kasa da kasa kan harkokin abinci da kayan halal a birnin Kualalampour fadar mulkin kasar Malazia a karo na shida, tare da halartar masana daga sassa daban-daban na kasashen musulmi da na larabawa da kuma na yankin Asia da suke da kyakkyawar dangantaka da kasashen musulmi.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zaman taro yana da matukar muhimmanci ga bangarorin da ke gudanar da ayyukan kasuwanci a cikin kasashen musulmi, da suke da dangantaka da harkokin kasuwanci da kasashen ketare, musamman ma ta fuskacin kasuwanci na kayan abinci.
Ana shirin gudanar da taron kasa da kasa kan harkokin abinci da kayan halal a birnin Kualalampour fadar mulkin kasar Malazia a karo na shida, tare da halartar masana daga sassa daban-daban na kasashen musulmi da na larabawa da kuma na yankin Asia.
762993