IQNA

Kungiyar Bunkasa Al’adun Kasashen Musulmi ISESCO Za Ta Gudanar Da Taro A Istanbul

16:05 - March 16, 2011
Lambar Labari: 2097086
Bangaren kasa da kasa, Kungiyar bunkasa harkokin al’adu ilimi na kasashen musulmi ta ISESCO ta dauki nauyin shiraya wani zaman taro na malaman makarantun addinin muslunci, wadanda suke koyar da harshen larabci, taron dai za agudanar da shi ne a birnin Istanbul na kasar Turkiya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kungiyar ISESCO an bayyana cewa, ministocin ma’aikatun bunkasa harkokin al’adu na kasashenmusulmi za su gudanar da wani zama a birnin Tilmisan na kasar Algeria, wanda cibiyar bunkasa al’adu ta kasashen musulmi ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a kasar ta Algeria.
Bayanin ya ci gaba da cewa, yanzu haka dai an fara gudanar da dukkanin shirye-shiryen da suka kamata domin daukar bakuncin wannan babban taro a kasar ta Algeria, wanda za afara gudanar kwanaki uku masu zuwa, tare da halartar jami’ai daga kasar.
Ministocin ma’aikatun bunkasa harkokin al’adu na kasashenmusulmi za su gudanar da wani zama a birnin Tilmisan na kasar Algeria, wanda cibiyar bunkasa al’adu ta kasashen ISESCO ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.
764077
captcha