IQNA

Za A Gudanar Da Taro Kan Wayar Da Kai Dangane Da Addinin Musulunci A Canada

23:06 - March 16, 2011
Lambar Labari: 2097164
Bangaren kasa da kasa, Ana shirin fara gudanar da wani zaman taro kan wayar da kan dangane da addinin musulunci da koyarwarsa akasar Canada, wanda za a gudanar a cikin wannan mako a jami’ar League Head da ke birnin Antario na kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na The Argus an bayyana cewa, ana shirin fara gudanar da wani zaman taro kan wayar da kan dangane da addinin musulunci da koyarwarsa akasar Canada, wanda za a gudanar a cikin wannan mako a jami’ar League Head da ke birnin Antario na kasar ta Canada.
Bayanin ya ci gaba da cewa kwamitin da ke kula da harkokin addinin musulunci na dalibai musulmi a jami’ar su ne suka shirya gudanar da wannan taro, inda za agudanar da laccoci da kuma raba makaloli da masana suka rubuta kan addinin musulunci da kuma koyarwarsa dangane da rayuwar al’umma ta zamantakewa.
Ana shirin fara gudanar da wani zaman taro kan wayar da kan dangane da addinin musulunci da koyarwarsa akasar Canada, wanda za a gudanar a cikin wannan mako a jami’ar League Head da ke birnin Antario na kasar.
764187




captcha