Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani zaman taro domin girmama wadanda suka yi shahada a boren da al'ummar kasar Bahrain ke yi domin neman sauyi a cikin harkokin siyasar kasar, wanda sojojin kasashen larabawa suke yi kisan gilla.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto dag shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, za a gudanar da wani zaman taro domin girmama wadanda suka yi shahada a boren da al'ummar kasar Bahrain ke yi domin neman sauyi a cikin harkokin siyasar kasar, wanda sojojin kasashen larabawa suke yi kisan gilla tare da hada baki da mahukuntan kasar.
Wannan zaman taro na daya daga cikin irin abubuwa da kuma bayanan yin Allawadai da manyan malaman addinin Musulunci na kasar Iran suka fitar a cikin 'yan lokutan nan da al'ummar musulmi na kasar Bahrain suke ganin kisan gilla daga sarakunan larabawan kasashen tekunfasha.
Za a gudanar da wani zaman taro domin girmama wadanda suka yi shahada a boren da al'ummar kasar Bahrain ke yi domin neman sauyi a cikin harkokin siyasar kasar, wanda sojojin kasashen larabawa suke yi kisan gilla ba gaira ba sabar.
765387