IQNA

Ayyukan Cibiyoyin Kur’ani Guda 25 A Yankunan Kudancin Birnin Tehhran

15:15 - March 24, 2011
Lambar Labari: 2097920
Bangaren siyasa da zamantakewa, a halin yanzu akwai cibiyoyi ashirin da biyar da suke gudanar da harkokin da suka danganci kur’ani mai tsarki a yankunan kudu maso yammacin birnin Tehhran fadar mulkin kasar Iran, wanda ayyukan nasu sun hada da isarda sakon musulunci da kuma wayar da kan mutane.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, bangaren yada labaransa na birnin Tehran ya bayar da wani rahoto dake cewa, a halin yanzu akwai cibiyoyi ashirin da biyar da suke gudanar da harkokin da suka danganci kur’ani mai tsarki a yankunan kudu maso yammacin birnin Tehhran fadar mulkin kasar Iran, wanda ayyukan nasu sun hada da isarda sakon musulunci da kuma wayar da kan mutanen yankunan.
A wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na lebanonfiles an bayyana cewa, babbar majalisar koli ta mabiya mazhabar iyalan gidan manzo a kasar Labanan ta yi kakkausar suka kan kisan gilla da mahukuntan kasar Bahrain suke yi wa masu gudanar da zanga-zangar cikin ruwan sanyi a fadin kasar.
Ayatollah Abdulamir Qabalan mataimakin shufgaban majalisar mabiya mazhabar shi’a a kasar Lebanon a cikin wani bayani da ya fitar ya kira ga mahukuntan kasar Bahrain da su yi amfani da hankali wajen warware koke-koken da mutane suke yi a kasar maimakon daukar matakan yin amfani da karfin tuwo wajen murkushe zanga-zangar da fararen hula suke gudanarwa.
Babbar majalisar koli ta mabiya mazhabar iyalan gidan manzo a kasar Labanan ta yi kakkausar suka kan kisan gilla da mahukuntan kasar Bahrain suke yi wa masu gudanar da zanga-zangar cikin ruwan sanyi a birninManama.
762190

captcha