Bangaren zamantakewa, shugaban cibiyar ilimi ta hauza a birnin Arumiyeh ya bayyana cewa, babbar manufar dokokin harkar kudi a addinin musulunci ita ce yin adalci a tsakanin mutane da kuma habbaka tattalin arzikinsu ba tare da danne hakkokinsu ba.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, banagaren yada labaransa na lardin Arumiyya ya habarta cewa, shugaban cibiyar ilimi ta hauza a birnin Arumiyeh ya bayyana cewa, babbar manufar dokokin harkar kudi a addinin musulunci ita ce yin adalci a tsakanin mutane da kuma habbaka tattalin arzikinsu ba tare da danne hakkokinsu ba ko cutar.
A wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Nasij an bayyana cewa, za aguudanar da wani zaman taro na kara wa juna sani kan mu’ujizar ilimin kur’ani mia tsarki da kuma sunnar manzon Allah (SAW) wanda za agudanar a karo na goma a birnin Istanbul fadar mulkin kasar Turkiya, tare da halartar masana daga sassa na kasashen duniya, musamman ma daga kasashen larabawa da na musulmi.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zaman taro an sabar gudanar da shi a kasar ta Turkiya, wanda ma’aikatar kula da ayyukan addinin musuluci ta kasar ta kan dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a kowace shekara, tun daga shekara ta dubu biyu da daya da ta gabata, inda masana kan gabatar da laccoci da kuma makalolin da suka tanada kan hakan.
764944