IQNA

Ya Rataya Kan Kafofin Sadarwa Su Mayar Da Martani Kan Farfagandar Makiya

17:44 - March 26, 2011
Lambar Labari: 2098099
Bangaren siyasa da zamantakewa, ya rataya kan kafofin sadarwa da su mike tsaye wajen kare matsayin cibiyoyin ilimi na hauza daga farfagandar kafofin yada labaran makiya, inda suka kwashe tsawon lokaci suna hankoron bata sunan hauza.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ta hada shi babban jami’i mai kula da harkokin koyarwa a cibiyar Hauza Muhammad Hassan nabavi ya bayyana cewa, ya rataya kan kafofin sadarwa da su mike tsaye wajen kare matsayin cibiyoyin ilimi na hauza daga farfagandar kafofin yada labaran makiya, inda suka kwashe tsawon lokaci suna hankoron bata sunan hauza a idon duniya.
A bangare guda kuma bayanin ya yi nuni da cewa an gudanar da wannan zaman taro ne da nufin kara karfafa mabiya addinin musulunci kan sanin addininsu da kuma tarihin manzo tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa, wanda hakan ne zai ba su damar yin aiki da koyarwa a cikin dukkanin harkokinsu na rayuwar zamantakewa.
An gudanar da wani zaman taro na mabiya addinin musulunci a yankin Rajuri na yankin keshmir, wanda ya samu halartar daruruwan malaman addini da kuma mutanen yankin wadanda akasarinsu mabiya addinin musulunci ne.
764214


captcha