Bangaren kasa da kasa, jami'an tsaron gwamnatin kasar Bahrain sun kunna wuta a cikin wasu masallatan kasar, tare da rusa wasu, bisa shirin da mahukuntan kasar tare da kawaynsu na yankin suke da shi na tayar da fitinar mazhaba a cikin kasar, bayan da al'umma suka nemi canji kan zalunci da suke fuskanta daga mahukuntan kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alkausar an bayyana cewa, jami'an tsaron gwamnatin kasar Bahrain sun kunna wuta a cikin wasu masallatan kasar, tare da rusa wasu, bisa shirin da mahukuntan kasar tare da kawaynsu na yankin suke da shi na tayar da fitinar mazhaba a cikin kasar, bayan da al'umma suka nemi canji kan zalunci da suke fuskanta daga mahukuntan kasar ta Bahrain.
Tun bayan da aka fara gudanar da zanga-zangar neman sauyi a kasar Bahrain, mahukuntan kasar wadanda 'yan sunna ne marassa rinjaye da suke shugabanci bisa tsari na sarauta kamar dai yadda 'yan mulkin mallakar Birtaniya suka shirya, sun nuna matukar kaduwa kan boren da al'ummar kasar suka yi, wadanda akasarinsu mabiya mazhabar shi'a ne, lamarin da ya sanya mahukuntan kasar kiran sauran takwarorinsu na saudiyya domin taimakonsu.
Jami'an tsaron gwamnatin kasar Bahrain sun kunna wuta a cikin wasu masallatan kasar, tare da rusa wasu, bisa shirin da mahukuntan kasar tare da kawaynsu na yankin suke da shi na tayar da fitinar mazhaba a cikin kasar, bayan da al'umma suka nemi canji kan zalunci da suke fuskanta daga mahukuntan kasar.
768401