Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a ranar sha shidda ga watan Farvardin shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in shekara ta hijira shamsiya a masallacin da ke tsakiyar garin Zaidpur a lardin Utarparadash na kasar Indiya aka gudanar da taron taimakawa al'ummar Bahrain da ake zalunta.Da misalign karfe goma na safiyar ranar ne aka fara gudanar da wannan taro tare da halartar malaman yankin da kuma musulmi masu yawan gasket na garin kuma an gabatar da jawabai da dama ga mahalarta taron.
769558